Ra’ayi: Allah ya jarabci Gwamnatin Talakawa na Baba Buhari, da Miyagun Sanatoci. Makiya Arewa da Najeriya

Ra’ayi: Allah ya jarabci Gwamnatin Talakawa na Baba Buhari, da Miyagun Sanatoci. Makiya Arewa da Najeriya

Kalubalen da gwamnatin talakawa karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke fuskanta daga Ahmadu Manage Bauchi

Majalisan dattawan Najeriya karkashin Jagoranci Sanata Bukola Saraki Dan Arewan da bayajin Hausa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya gayyato likitocinsa Najeriya, ya fasa komawa Asibitin Landan

''Tun dawowar mulkin demokaradiyya kasan mu Najeriya a 1999, babu wata Gwamnati a kasan mu Najeriya da ke shan bakar azaba, da musgunawa da kyama da tozarci da Cin mutunci da munafunci, da kiyayya kaman wannan Gwamnatin na talakawa wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ke mata jagoranci.

''Kamun zuwan wannan Gwamnatin na Baba Buhari, Gwamnatocin baya sun kasance Gwamnatoci ne na sata da warwaso da dukiyan kasa da zubar da jini amma basu taba fiskantan wata matsala da Majalisan kasa ba hasalima suna zaune lafiya lafiya, da wainnnan mutanen.

"Amma abun bakin ciki da takaici shine daga lokacin da wannan Gwamnati na Talakawa wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranci tazo kan karagan mulkin kasan nan wainnnan mutanen suka saka wannan Gwamnatina gaba suna kukarin ganin sun ruguza dukkan niyyan ta na Alkhairi.

"Duk da cewa dayawa daga cikin Sanatocin Najeriya musamman ma wainnnan sanatoci namu na arewa mun kai su wannan Majalisan ne domun maraya ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari, domun Gwamnatin sa tayi nasara.

''Hasalima wainnnan mutanen basu kashe komai ba a lokacin da muka kai su Majalisan kasa hasalima sun tafi ne a Guguwan Buhari, mu mutanen Bauchi kowa yasan kanda muka gudanar da zaben mu a wannan zaben data gabata duk wanda ya fito a jamiyan APC na Baba Buhari, mun bashi dama a Jihar Bauchi yaci ba tare da ya ji ko ina yakin neman zabe ba.

"Wasu ma daga falon su sukaci zabe musamman ma su wainnnan sanatoci namu na Jihar Bauchi wanda aka gudanar da zaben su rana daya dana Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

''Yau Sanatocin Najeriya musamman ma Jagoran su Shugaban Majalisan dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki, Dan Arewan da bayajin Hausa, sun dauki makamai na yaki a Majalisan kasa domun ruguza dukkan niyyan Alkhairi da wannan Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta shirya ta tsara Domun inganta rayuwan Talakawa Najeriya.

"Ga manya manyan aiyukan da yakamata Majalisan dattawan Najeriya suyi amma sun kama sun tsaya fada da Talakawan Najeriya domun dukkan aiyukan da Baba Buhari, keyi yanayin sune ma yan Najeriya ba irin Sanatocin mu ba masu yi ma kansu.

"Inhar da wainnnan mutanen kasan mu Najeriya suke kishi ai da sun bawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari dama ya nada Ibrahim Magu, domun cigaba da yaki da Cin hanci da Rashawa a Najeriya.

'Inhar da wainnnan mutanen cigaban Najeriya sukeyi da sun kira Hamid Ali, Shugaban hukumar kwastom sun bashi lamban yabo na kasa saboda irin gudumawan da yake bawa kasa wurin habaka tattalin arzikin Najeriya Kasancewar babu wani Shugaban Kwaston nan kusa da ya tara kudin shiga ma Najeriya kaman kanda Hamid Ali, ya tara.

'Inhar da wainnnan mutanen cigaban Najeriya sukeyi da sun dauki Matakinyin dokoki a Najeriya dokokin da dasu kawo karshen mulkin kama karya da ake cigaba da gudanar a kananan hukumomin Najeriya.

"Dukkan matsaloli yan Najeriya ba damuwan Sanatocin mu bane domun yau inhar ka dauki Maganan Zaben Kananan hukumomi wanda yaki yaki Cinye wa.

"kamata yayi Majalisan dattawan Najeriya tayi dokokin da dai kawo karshen zaman kananan hukumomin Najeriya 774, a hannun Gwamnoni Kasancewar yau zaman su a hannun Gwamnoni ba Alkhairi bane.

"Amma sun kasa ga aikin da babu Talakan Najeriya da baya bukatan yau ace kananan hukumomin Najeriya suna da Yancin Cin gashin kansu amma su wainnnan mutanen ba damuwan Talakawa babe a gaban su su damuwan su shine.

"Kada Gwamnatin Talakawa na Buhari, tayi nasara bukatan su shine ayita tafiya haka tunda su Shugaban su Sanata Bukola Saraki Dan Arewan da bayajin Hausa, yana son Shugabancin Najeriya tam di jam.

"Matasan Najeriya musamman ma na arewa wannan fada fa damu akeyi lokacin da Obasanjo da Jonathan, suke mulki sun samu irin wannan Matsala da Gwamnatin Talakawa na Buhari, ke samu amsa shine basu samu ba.

"Yau Yan Majalisan dattawan Najeriya na Arewa sun fi yawa amma yawan banza.

"Allah muna rokon ka da sunayen ka masu tsarki 99, Allah ka ruguza Shirin makiya Gwamnatin Talakawa na Buhari.

"Allah ka bawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari hikima da basiran ciyar da kasa gaba. Ka kara ma Baba Buhari lafiya da nisan kwana Mai Alkhairi, ka bawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, nutsuwa."

"Mutashi mu farka Yan Arewa Wannan abunda da ke faruwa anayi ne kawai domun Ruguza aiyukan Gwamnatin Talakawa na Buhari, musamman ma a Arewa ana hada baki da Yan Arewa Domun kawo Cikas ma Gwamnatin Talakawa na Buhari.

"Yau hako Man Fetur a Bauchi da Borno yayi nesa.

"Ya Allah ka ruguza Shirin makiya Gwamnatin Talakawa na Buhari. Allah ka bawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari hikima da basiran ciyar da kasa gaba.

"Allah ka ruguza Shirin makiya Gwamnatin Talakawa na Buhari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kunyi danasanin zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari?

Asali: Legit.ng

Online view pixel