Hukumar alhazai ta sanar da rage kudin hajjin bana

Hukumar alhazai ta sanar da rage kudin hajjin bana

- Hukumar kula da aikin Hajji ta Kasa ta sanar da rage kudin gidajen da mahajjatan bana za su biya a lokacin aikin hajji.

- Hukumar ta ce hakan ya yiwu ne bayan tattaunawa da tayi da masu gidajen da take shirin kamawa ‘yan Najeriya a hajjin bana.

Maniyyata aikin hajji
Maniyyata aikin hajji

Kakakin hukumar Uba Mana ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da hukumar ta fitar yau kuma jaridar Legit.ng ta samu labari.

A dalilin haka mahajjata zasu biya kasa da riyal 500 zuwa 900 a garin Makka sannan kuma su biya kasa da riyal 614 a Madinah a hajjin 2017.

KU KARANTA: An kaiwa daliban Najeriya hari kasar India

Yace za’a samu ragin sama da Dala Miliyan $12 ganin tattaunawar da sukeyi akan hakan a gidajen Madinah.

Uba yace zasu biya kudaden gidajen ne bayan sun tabbatar da kyan gidan da kuma kusancinsa da harami bakamar yadda akeyi da ba ace wai ga kayyadadden Kudi da za’a biya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli yadda mutanen garin Daura a jihar Katsina suka nuna farincikin su da dawowar Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel