Fina-Finan Hausa na wannan karnin, basa nuna al'adun malam Bahaushe
Jarumar wasan Hausa, da ta ga jiya ta ga yau a harkar fina-finan Hausa, Hauwa Haruna, wace aka fi sani da ‘Ladin Cima’ ko ‘Tambaya Matar Malan Mamman’ ta yi tsokaci a kan harkan shirya fina-finai a baya da yanzu.
Jarumar ta bayyana cewa harkar fim a da, da yanzu akwai bambanci sosai, domin kuwa ana nuna tsantsar dabi’un malam Bahaushe ne, na kunya da al’adu da suka kamata, inda bai yuwa a nuno mata da miji a cikin daki daya.
KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Buhari ya tsige daraktocin tarayya 5
Ta ce amma yanzu zamani ya zo, da har ana nuno su tare a kan gado, baya ga shigo da wasu yaruka daban da aka hada a fina-finan malam Bahaushe, wanda hakan ya tabbatar da cewar, ba al’ada ake nunawa ba, don kuwa mafi akasari al’adun kasashen waje ake nunawa, na zamani masu kyau da marasa kyau.
Mu tuna cewa a kwanakin baya Legit.ng ta kawo rahotanni kan jarumar kamfanin shirya fina-finan Kannywood, Rahma Sadau da aka dakatar, sakamakon yanayin da ta a wani waka tare da mawaki Classiq, wanda ake ganin ya saba ma dokar shirya fina-finai.
Kalli bidiyon hira da Legit.ng tayi da yan wasan barkwanci:
Asali: Legit.ng