Babachir David Lawal ya wanke kan sa daga zargi

Babachir David Lawal ya wanke kan sa daga zargi

– Sakataren gwamnatin tarayya ya wanke kan sa daga zargin da ake masa

– Ana zargin Babachir da bada kwangilolin bogi da dama

– Mista Babachir Lawal ya karyata wannan zargi yace yana da gaskiya

Babachir David Lawal ya wanke kan sa daga zargi
Ina da gaskiya-Babachir David Lawal

Sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal ya wanke kan sa daga duk wani zargi da ake yi masa na cewa ofishin sa ya bada wasu kwangiloli ga kamfanin karya wanda aka yi gaba da wasu makudan kudi.

Babachir ya bayyana cewa duk kwangilar da aka bada sai da aka bi ka’ida sarai yadda ko shi Sakataren gwamnatin ba zai iya yin abin da bai dace ba don ma ba ya cikin kwamitin da ke bada kwangila a kasar. Bolaji Adebiyi wanda shi ne Jami’in yada labarai na ofishin Sakataren gwamnatin ya bayyana haka.

KU KARANTA: Fashola ya gana da Ambode bayan dogon lokaci

Babachir David Lawal ya wanke kan sa daga zargi
Ana zargin Babachir David Lawal da handame wasu kudi

Majalisa dai tana zargin Mista Babachir Lawal da handame wasu kwangila na aikin fitiki a yankin Arewa maso gabas. Tuni dai Mista Babachir yace Hukumar PINE mai kula da wannan aiki za a rike ba shi don kuwa shi bai san komai ba.

Sanata Shehu Sani wanda shi yayi wannan bincike yace yanzu an yi jana’izar yaki da cin hanci da rashawa a Gwamnatin Shugaba Buhari. Don kuwa ana tsince wadanda za a bincika ne da laifi a Mulkin na Buhari tun da na kusa da shi irin su Babachir duk sun sha.

Ku same mu a Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa ko kuma Facebook https://www.facebook.com/naijcomhausa

Yadda DSS ta tsare iyalan wasu Jama'a

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng