Kyawawan hotunan farko daga auren ‘yar Amina Mohammed
Misis Amina J. Mohammed, mataimakiyar sakataren majalisar dinkin duniya na yanzu ta haska a gurin bikin auren yar ta Nadine da akayi kwanan nan.

'Yar Misis Amina J Mohammed mai tsananin kama da ita Nadine ta fara liyafar bikin ta a ranar Alhamis sannan kuma wannan ne hotunan farko daga bikin.
KU KARANTA KUMA: Wayyo! Ana nema a kashe ni Inji Hadiza Bala Usman
Hukumar Legit.ng tayi murnan ganin Misis Mohammed kusa da matar mataimakin shugaba kasa Osinbajo yayinda suke walwala da juna.

KU KARANTA KUMA: Yadda muka gano dukiyoyin Alex Badeh – EFCC

An gano Nadine sanye cikin kayan alfarma yayinda take zagayawa a gurin bikin ta. Tana dauke da murmushi a kan fuskarta wanda ba abun mamaki bane saboda tace tana auren burin ranta.

Muna taya su murna!
Kafin ma’aurata suyi aure, akwai abubuwa da dama da ya kamata suyi tunani a kai sannan a bidiyon kasa, wasu yan Najeriya sunyi magana da Legit.ng kan shekaru a aure:
Asali: Legit.ng