DA DUMI-DUMI: Shugaba Buhari yayi sabon nadi

DA DUMI-DUMI: Shugaba Buhari yayi sabon nadi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sababbin mukamai dazu-dazun nan ba da dadewa ba kamar yadda muke samun labari a ma’aikatar noma

DA DUMI-DUMI: Shugaba Buhari yayi sabon nadi
Shugaba Buhari yayi sabon nadin mukamai

Shugaba Muhammadu Buhari nada sababbin shugabanni da Darektocin Bankin manoma na kasar da ake kira BOA. Ma’ikatar noma da raya karkara ce dai ta bayyana wannan nadi da aka yi a yau Alhamis dinnan.

Lere Adams-Blessing Mataimakiyar Darektan yada labarai na Ma’aikatar noma ta fitar da wani jawabi inda take bayyama cewa shugaba Buhari ya nada Mohammed Kabiru a matsayin shugaban bankin noma na rikon kwarya.

KU KARANTA: Dan Majalisa ya tona asirin Coca Cola

DA DUMI-DUMI: Shugaba Buhari yayi sabon nadi
Ministan gona Audu Ogbeh

An dai kuma nada sababbin Darektoci na bangarorin da ake da su. Darektocin dai su ne dai; Dr. Okenwa Gabriel, Aweh Owoicho da kuma Bode Abikoye. A jawabin dai ake cewa nadin zai taimaka wajen samun kudi domin harkar noma.

Da safiyar yau kuma ‘Yan kasuwa masu canjin kudi su ka fara kokawa da lamarin yayin da darajar Dala ya kara yin kasa. Idan ba ayi sa’a ba ma dai abubuwan na iya kara tabarbare masu nan gaba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng