Su wa suka fi kowa kudi a Najeriya?

Su wa suka fi kowa kudi a Najeriya?

– Alhaji Aliko Dangote shi ne mai kudin Najeriya da ma Afrika gaba daya

– Mike Adenuga ne ke bayan Dangote a kasar nan

– Ko kana da labarin wata mata Folorunsho Alakija?

1. Aliko Dangote

Aliko Dangote
Aliko Dangote kenan in dai kudi ake magana

Rahotanni da ke fitowa na wannan shekarar daga Mujallar Forbes sun nuna cewa Alhaji Aliko Dangote ya fita daga cikin sahun mutane 100 da suka fi kowa kudi a Duniya. Amma duk da haka shekara 6 kenan dai har yanzu babu wanda ya kai Aliko Dangote dukiya a kaf Nahiyar Afrika ba ma Najeriya ba. Dangote ya ba Dala Biliyan 12 baya.

KU KARANTA: Dangote yayi kasa a masu kudin Duniya

2. Mike Adenuga

Mike Adenuga
Mike Adenuga mai GLO kasurgumin Attajiri ne

Adenuga ne mai rike da kamfanin GLO kuma shi ne na biyu a bayan Dangote in dai kudi ake magana a Najeriya. Adenuga mai shekaru 63 ya mallaki sama da Dala Biliyan 5.8. Adenuga ne dai na 250 a cikin masu kudin Duniya.

3. Folorunsho Alakija

Su wa suka fi kowa kudi a Najeriya?
Folorunsho Alakija Attajirar Duniya

Ina ka baro Folorunsho Alakija? Ka ji manyan mata! Ba ma Najeriya ba, duk Duniya da wuya a samu bakar mace da ta kera Alakija kudi. Shekarun baya dai ta zarce Attaajira Oprah Wimfrey ta Amurka. Alakija mai shekaru 66 ta tsunduma ne a harkar mai ta kuma mallaki sama da Dala Biliyan guda.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng