An fallasa wani babban sirrin Sanata Dino Melaye (Karanta)

An fallasa wani babban sirrin Sanata Dino Melaye (Karanta)

Yanzu haka dai wata wutar rikice ta fara ruruwa a fannin siyasar Sanatan nan dan rigima daga jihar Kogi watau Dino Melaye inda rahotanni suke nuna cewa korar shi ma akayi daga jami'a.

An fallasa wani babban sirrin Sanata Dino Melaye (Karanta)
An fallasa wani babban sirrin Sanata Dino Melaye (Karanta)

Gidan jaridar nan na Sahara Reporters ne dai ya fallasa wannan bayanin ida suka ce babu sunan Dino Melaye a cikin jerin sunayen wadanda suka kammala karatun su a jami'ar ta ABU dake Kaduna sabanin yadda yake cewa a can ya gama din.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Sako daga Shekau

Rahoton binkicen ya kuma kara da cewa tuni har an tura ma hukumar DSS da wannan zargin amma sai sukayi kunnen uwar shegu da zancen inda har yanzu basu bincika ba.

Shi dai Dino Melaye yana daya daga cikin yan amutun shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki kuma kawo yanzu yana cikin rikice-rikice da dama da suke faruwa a majalisar ta dattijai musamman ma yadda ya dage kan lallai ba zasu tantance shugaban hukumar EFCC ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel