Ta kama karuwar mijin ta, sai tayi mata wannan mummunan hukuncin (Hotuna)
1 - tsawon mintuna
Wata mata dake zaune a garin Calabar dake a jihar Cross Rivers a can kudancin Najeriya ta fallasar asirin karuwar mijinta yayin da ta watsa hotunan ta a saman titunan garin.
Ita dai wannan mata ta dauki wannan mummunan mataki ne bayan da ta gano cewa ashe akwai wata yarinya dake bin mijin ta. Matar sai ta yi kokarin nemo hotunan ta ta kuma buga su a jikin manyan takardu sannan kuma ta mammansu a titunan Calabar babban birnin jihar ta Cross Rivers.
Haka zalika ga abun da matar ta rubuta a tare da hoton karuwar: "Jama'a ga fa mai shiga tsakanin ma'aurata. Sunan ta Mary Agida. Ina rokon ta da ta fita harkar mijina ta je ta samo nata."
Abun dariya. Ko me kuka tunani game da hakan?
Asali: Legit.ng