Ashe Malam Nasir El-Rufa’i butulu ne?

Ashe Malam Nasir El-Rufa’i butulu ne?

– Gwamnan Kaduna El-Rufa’i ya rubuta wasika ga shugaba Buhari

– Malam El-Rufa’i ya kira shugaba Buhari yayi gyara

– Wani na kusa da Jonathan yayi tir da halin El-Rufa’i

Ashe Malam Nasir El-Rufa’i butulu ne?
Ashe Malam Nasir El-Rufa’i butulu ne?

Kwanan nan aka samu labarin cewa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya rubuta wata wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yake kiran sa da yayi maza yayi wasu gyara a mulkin sa.

Wani mai ba tsohon shugaban kasa Jonathan Goodluck shawara a wancan lokaci watau Mista Reno Omokri yayi kaca-kaca da El-Rufa’i inda ya kira sa Munafuki. Omokri yace haka El-Rufa’i yayi wa sauran manyan sa irin su Tsohon shugaban Obasanjo da Atiku Abubakar.

KU KARANTA: Da gaske za a tsige El-Rufa'i?

Reno Omokri yace bai dace Gwamna El-Rufa’i ya fallasa shugaba Buhari a bainar Jama’a ba. Mista Omokri yace sai dai El-Rufa’i yayi abin da ya saba ne don haka yake dabawa mutane wuka bayan sun yi masa rana.

Jama’a dai suna ta yada rade-radin cewa an wuce da Gwaman Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i Turai zuwa asibiti a sakamakon rashin lafiya da ke damun sa. Wasu kuma suka yi ta yada cewa ana shirin tsige Gwamnan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng