Nan da wata uku za'a fara fitar da man fetur a jihar Bauchi

Nan da wata uku za'a fara fitar da man fetur a jihar Bauchi

Sama da shekaru ashirin 20 ne masana suka tabbatar da cewar kauyen Baranbo dake Karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi akwai danyen man fetur malale a wajen, wanda Allah Ya azurta Nijeriya da shi. A bisa haka ne Ma’aikatar Man Fetir ta kasa, NNPC ta kudiri aniyar hako danye man da kuma binciken man a wannan kauyen inda aka fara aikin a watannin baya.

Nan da wata uku za'a fara fitar da man fetur a jihar Bauchi
Nan da wata uku za'a fara fitar da man fetur a jihar Bauchi

A makon jiya ne Gwamnan Jihar Bauchi ya kai ziyarar gani da ido wajen da ake aikin hako danyen man fetur din, inda ya bayyana jin dadinsa da yadda ya ga aikin ke tafiya ka’in da na’in. Ya kuma bada tabbacin cewar Nijeriya za ta ci moriyar wannan aikin ta fuskoki da daman gaske.

“Ahmadullahi a kokarin habaka Nijeriya ne ya sanya gwamnatin Nijeriya da ita Ma’aikatar Mai NNPC da karamin kamfaninta na IDSL suka himmatu wajen ganin sun yi nasarar wannan aikin. Inda a yau muka gane wa idonmu manyan na’urorin da suke amfani da su wajen wannan aikin na hakko danyen man. A dalilin haka ne ya kama mana tilas mu ‘yan wannan al’umman mu ba su goyon bayan da duk ta dace don samun nasarar da aka sanya a gaba.”. in ji Gwamnan.

KU KARANTA: Sule Lamido ne zabin mu a 2019 - Kungiyoyin APC

Da yake nasa jawabin, Shugaban Hukumar Mai ta Kasa NNPC, Maikanti Baru ya bayyana cewar sun yi wa aikin shiri na musamman wanda sun kawo na’o’iri da manyan kayan aiki don ganin sun kai ga samo man fetur din.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Babban Manajan Gamayya na Frontier Ddploration Serbices, Dakta Mazadu Bako ya ci gaba da cewa Nijeriya za ta ci moriyar aikin fiye da yanda ake tsammani.

A cewar ta hukumar ta NNPC, nan da wata uku za mu fitar da sakamakon aikin.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng