Wasu yan mata guda 2 daga kabilar Igbo sun musulunta
Wasu matasan yan mata guda biyu yan kabilar Igbo daga Mbaise dake jihar Imo sun shiga addinin mususlunci.
Yan matan wadanda suka canja sunayensu zuwa na musulmai wato Zainab da Halimah sun kammala karatu daga makarantar Darus-salam.
A cewar shafin Facebook din Islamic Calling Family yan matan sun kammala karatunsu a jiya Laraba, 15 ga watan Maris.
KU KARANTA KUMA: Dalibar makaranta ta rasa idonta bayan harin da malami ya kai mata, amma kwararru sunce naira miliyan 1 zai iya dawo da ganinta
Islamic Calling Family ta rubuta a shafin ta na Facebook: “Wannan aikin Islamic Calling Family ne...
“Zainab da Halimah daga Mbaise sun kammala karatu daga makarantar Darus-salam jihar Kaduna a yau 15 ga watan Maris 2017. Alhamdulillahi yanzu suna da ilimin addini.”
Kalli bidiyo a kasa:
Asali: Legit.ng