Hotunan ziyarar da Kwankwaso ya kai garin Ile-Ife
Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma Sanatan al’ummar Kano ta tsakiya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara garin Ile Ife na jihar Osun, don jajanta ma al’ummar kabilar Hausawa dake jihar biyo bayan wani rikici daya kaure tsakaninsu da yarbawan garin.
Kwankwaso ya kai ziyarar ne don gane ma idanunsa matsayin halin da Hausawa mazauna garin Ile-Ife suke ciki, sakamakon rikicin daya faru a satin daya gabata inda aka kashe sama da mutane 25 yan kabilar Hausa.
KU KARANTA: ‘Ɗan N50m ɗin da Makarfi ke samu a hannun gwamnoni ne yasa bai son sulhu a PDP’ – Modu Sheriff
Kwankwaso ya samu ganawa da gwamnan jihar, Rauf Aregbesola, da shuwagabannin Hausawa mazauna garin. Tare da basu tallafi.
Ga sauran hotunan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng