Zeenat Zakzaky ta rubuta budaddiyar wasika ga Buhari

Zeenat Zakzaky ta rubuta budaddiyar wasika ga Buhari

Zeenat ta kasance matar shugaban musulman Shi’a na Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ta runbuto budaddiyar wasiga ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sakamakon wani karo ya afku tsakanin yan Shi’a da hukumar sojin Najeriya, ma’auratan biyu na tsare bisa ga umurnin shugaban kasa, duk da cewan kotu ta bayar da umurni a sake su.

Zeenat ta rubuto wani wasika dauke da dukkan abubuwan da ya faru tun daga gwamnatin Jonathan har zuwa gwamnati mai ci.

Ga wasikar kamar haka:

Ya kai shugaban kasa,

Ina gaishe ka yayinda kake gutu a birnin Landan. Gaisuwata da fatan ailkhairi gare ka da masoyanka dake kula da kai a lokacin da kake bukatar hakan. Ina roka maka gafarar Allah a kan ka.

Ranka ya dade, shin ka tuna watan Yuli na shekarar 2014? Na tabbata ka tuna abubuwan bakin ciki a watan Yuli 2014. Wata ne da kaddara ya hada mu a al’amarin bakin ciki da rayuwa.Yuli 2014 ya kasance watan da Najeriya ta daga sakamakon yunkuri da akayi na daukar ranka a tashin bam da yayi sanadiyan mutuwar kusan mutane dari da basu san hawa basu san sauka ba.

Wannan watan ya kasance lokaci da Allah yayi maka aikin gafara ya cece ka. Watan Yuli 2014 ya kuma kasance watan da hukumar sojin Najeriya karkashin shugaban kasa Goodluck Jonathan suka kashe masi ‘ya’yana guda uku a cikin musulmai 35 dake gudanar da hakkinsu na taruwa. Kaddara ta hada mu a wannan watan yayinda yan Najeriya suka bayyana cewa bazasu yarda ba.

Gwamnan jihar Kaduna mai ci a yanzu, Nasir el-Rufai, ya mika ta’aziyyarsa ga mijina.

Zeenat Zakzaky ta rubuta budaddiyar wasika ga Buhari

Ba wai El-Rufai na nuwa zuga mutane kan abunda sojoji ko gwamnatin Jonathan sukayi bane, kawai dai yana fadin gaskiyar bakin cikin da nake ciki ne kamar yadda yake hakkinsa kuma yan Najeriya bazasu iya ci gaba da jure ma haka ba. Su suka zabe ka.

Ranka shi dade shugaban kasa Muhammadu Buhari, a matsayinka na shugaban Najeriya wanda Allah ya daura ma nauyin yin adalci ga mutane miliyan 180, har yanzu baka hukunta gwamnatin Jonathan kan wannan kisan kiyashin da Nasir el-Rufai ya tabbatar da laifin su ba.

Sannan a yayinda muke jira don ganin ka yi adalci a kanmu kamar yadda ya ta’allaka a wuyar ka, kana bun bakin cikin watan Yuli 2014 na kisan gillan da akayi ma ‘ya’yana, maimakon haka a watan Disamba na shekarar da ta biyo, hukumar soji karkashin shugabancin Janar dinka, Tukur Buratai ta yi kisan kiyashi ga sama da musulmai 1000 a fadin Zaria bayan wasu matasa sunyi zanga-zanga sannan suka toshe hanyar sa. Bugu da kari, hukumar soji ta ci zarafin ‘ya’yanmu mata, ta kona musulmai da dama a raye yayinda suka halaka dukiyoyinmu a fadin unguwanni shidda a Zaria. Sojojinka basu tsaya a nan ba, suka tayar da gidan mu a kanmu sannan suka kona shi. Lokacin da suka gano ni da sauran ahlinmu boye a bandaki, Allah ne ya cecemu da tankar ruwan zafin da ke kashe wutan; suka harbe dukkanmu sannan suka kuma kashe ‘ya’yana maza guda uku a kan idanu na.

A karkashin kulawar ka gwamnatin Kaduna da hukumar soji karkashin umurnin Buratai, a cikin dare, cikin sirri suka je suka binne musulmai 1000, maza, mata da kananan yara, yawancinsu suna raye a katon rami a makabartan Mando.

Tun lokacin sojojinka, hukumar DSS da gwamnatin jihar Kaduna ke tsare da yawancin mu sama da shekara day aba tare da chaji ba. An ji mana raunuka da bindiga ni da mijina wanda a yanzu yake fama da mutuwar barin jiki daya da makanta, kun tsare mu tun lokacin sannan kun take mana hakkinmu duk da umurnin kotu.

Bamu da lafiya, mun karairaye koda dai bamu cire tsammani da Allah ba. Bamu sami ganin yan uwanmu ba, mun rasa auren dan mu. Ya kai shugaban kasa Muhammadu Buhari. Me yasa ka rufe ni haka? Mai nayi da na cancanci wannan? Allah ya albarkace da damar da kuma asusun Najeriya da jiragen shugabanci don ka dunga tafiya birnin Landan sannan ka samu kulawar likitoci mafi inganci a duniya duk tsadar sa. Muna godiya ga Allah da ni’imomin sa.

Abunda kawai na ke burin sani shine dalilin da yasa ka fi karfin doka sannan kuma baka bin dokar da kotu ta bayar, na cewa ka sake ni don na samu na rungumi da na guda daya da ya rage sannan kuma na rungume ‘ya’yana mata guda biyu?

Allah ya yi maka aikin gafara sannan ya baka tsawon rai. Ya kuma kare ka da ‘ya’yanka daga wahalar da muka fuskanta a hannunka da na Jonathan. Allah ya yafe maka.

An kama El-Zakzaky da matarsa shekara daya da ya wuce (ranar 5 ga watan Disamba, 2015) bayan wani karo tsakanin yan kungiyar Shi’a da rundunar shugaban soji Tukur Buratai a Zaria, jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel