Ina so na mutu, dukka yarana sunyi watsi da ni – tsohuwa mai shekaru 85 ta koka (HOTO)

Ina so na mutu, dukka yarana sunyi watsi da ni – tsohuwa mai shekaru 85 ta koka (HOTO)

Wata tsohuwa mai shekaru 85, Bolaji Isaac, ta koka kan cewa tana so ta mutu saboda bata ga dalilin kasancewarta a raye ba.

Isaac ta bayyana cewa dukka ‘ya’yanta guda biyar sunyi watsi da ita kuma duk kokarinta na son ganin su a banza wannan ne yasa take fatan ta mutu. Ta kara da cewa zata tafi kabarinta da bakin ciki da dacin rai.

Ina so na mutu, dukka yarana sunyi watsi da ni – tsohuwa mai shekaru 85 ta koka (HOTO)

Tace dan ta na biyu mai suna Sola, ya tursasa ta barin gidanta da wani coci a Lagas ta yi mata haya.

Matar wacce ta kasance yar asalin jihar Ondo tayi bayanin cewa tana tsananin bukatar gurin zama, ta roki yan Najeriya da su taya ta fada ma ‘ya’yanta da su zo gareta kafin ta mutu.

KU KARANTA KUMA: Fayose ya ziyarci tsohon shugaban kasa Abdulsami Abubakar (HOTUNA)

Tace: “Ina da ‘ya’ya 10. Yayinda guda biyar suka mutu, biyar sun rayu. Mijina ya mutu kimanin shekaru da suka wuce sannan na fara siyar da jakunkunan takarda a asibitoci da guraren kiwon lafiya. Lokacin da kudi yak are mun na wannan aikin, sai na daina.”

“A da ina zaune a Alagbado dake jihar Lagas, amma da na, Sola, yak ore ni. Ya zo daga jihar Ondo don ya zauna da ni.

“Matar sa ta kira ni cewa na koro shi ya koma. Amma na share ta. Daga baya, na yarda da matsin yayi yawa. Lokacin da na bukaci ya dawo, sai yaki sannan ya fara fada dani.”

Ta ci gaba da cewa duk lokacin da ta kira dan ta na hudu, Samuel, wanda ya kasance Lauya, sai ya dunga bata uzurin cewa yana kotu. Tace Samuel ma ya ki bari ta san gidan sa.

Tace: “Lokacin da nake da kudi, mahaifiyata na banin shawaran cewa na kula dasu cewa su zasu kula da ‘ya’yana a nan gaba. Ni na dauki nauyin karatunsu, amma yanzu basu kula dani. Ban san me nayi ba da nake fuskantar wannan wahalar. Ina so na mutu. Bazan iya jure ma wannan wahalar ba.”

Isaac twacce tace ta dogara ne da taimakon naira dubu biyu (N2,000) da take samu daga kungiyar MFM a duk ranar Litinin tace ta koma zama da wata kawarta.

A cewar jaridar Ounch, dan ta, Samuel, wanda ya kira a kan waya ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta cika rigima, ya kara da cewa ya nisanta ta daga iyalansa ne saboda guje ma matsaloli a auren sa.

Allah ya kyauta!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng