Kungiyar Izala ta caccaki dokar ƙayyade aure da Sarki Sunusi ke neman ƙirƙirowa

Kungiyar Izala ta caccaki dokar ƙayyade aure da Sarki Sunusi ke neman ƙirƙirowa

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'a Wa'ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa reshen Jos tayi watsi da dokar kayyade auren mata sama da daya a tsakanin talakwa wanda Sarkin Kano mai martaba Muhammadu Sunusi II ke kokarin samarwa tare da tabbatar da ita a jihar Kano.

Kungiyar Izala ta caccaki dokar ƙayyade aure da Sarki Sunusi ke neman ƙirƙirowa
Sheikh Jingir

Shugaban kungiyar reshen jihar Jos Sheikh Sani Yahaya Jingir ne ya tabbatar da haka yayin dayake jawabi a garin Jos.

A cewarsa musulunci ya bayyana karara a cikin Qur’ani cewar mutum na da daman auren mace daga daya zuwa hudu idan yana so, ya kara da cewa dokar zata tauye ma maza hakkinsu na kara aure.

KU KARANTA: Idan maigidanki ya mare ki, ki rama — Sarki Kano

Jingir yayi kira ga Sarkin daya fadada neman shawara tare da tattaunawa da sauran manyan malaman musulunci don samar da ingantattun hanyoyin magance matsalolin da suka dabaibaye lamurran aure a yankin Arewa.

Sheikh Jingir ya cigaba da fadin “duba da yawan mata da suka rasa mazajensu sakamakon yakin Boko Haram bai kamata a tabbatar da dokar nan ba” inda yace dokar zata kuntata ma ire iren matan, saboda rashin mataimaka.

Daga karshe Jingir ya janyo hankalin maza ma’aurata dasu ji tsoron Allah su tabbata suna sauke hakkin aure dake kawunansu, inda yace kowa sai ya bada bahasin rayuwarsa a ranar gobe kiyama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng