Ku sadu da Danliti: Dan arewan da zai kera kera na’aurar lantarki mai amfani da hasken wata
- Wani matashi dan shekara 15 kuma mazaunin Karamar Hukumar Kura da ke jihar Kano mai suna Danliti Ciliti yace yana gab da kammala kera wata na’auran tara wutan lantarki mai amfani da hasken wata
- Ba kamar yadda kowa ya sani cewa na’urori masu amfani da hasken rana ce kawai ake gani kuma ake mu’amula da su, Danliti yace shi nasa na’uran da yake kirkirowa da hasken wata ce za ta yi amfani
“Banga sana’ar da zata gagareni ba da yardar Allah. Allah shiyasan yawan sana’oin da na iya.”
Danliti yace ya kirkiro abubuwa da dama kamar su rediyon kwali, ya iya gyarankwan fitillan da ta mutu, ya iya zana gida kowanne iri da ginawa, shi kafinta ne kuma yana gyaran karaya ko targade.
“Ina gyaran Keke Napep wato adaidaita sahu, ni kafinta ne, ni makaniken mota ne sannan ina gyaran keken dinki.''
KU KARANTA: Musulmai sun hada kudi don gyara makabartar Yahudawa
Danlami yace wannan baiwa ce Allah ya bashi a garin kura kuma kowa ya sanshi da sana’o’insa.
Yace a yanzu yana ci gaba da nazarin kera na’urar tara wutan lantarki amfani da hasken farin wata wacce sam baza tayi aiki da hasken rana ba da izinin Allah.
Yanzu hakan Danliti ya gano yadda za’a gyara memori na waya.
Kamar yadda ya fadi, Danliti yace ya gano hakanne saboda hasarar da mutane sukeyi idan memori din wayarsu ta lalace. Yanzu yana gyara memori kuma ta dawo aiki kamar yadda take ada.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa
Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng