Abin mamaki ya faru a Duniyar kwallon kafa

Abin mamaki ya faru a Duniyar kwallon kafa

– Kungiyar Leicester ta raba jiha da Kocin ta Claudio Ranieri

– Ranieri ya ci wa Leicester Kofin Firimiya a bara

– Sai dai bana abubuwa sun sukurkucewa Leicester

Abin mamaki ya faru a Duniyar kwallon kafa
Abin mamaki ya faru a Duniyar kwallon kafa

A shekarar bara ne dai Kungiyar Leicester City ta Ingila tayi abin da kusan ba a taba yi ba a Duniya. Leicester City ta lashe Gasar Firimiya na Ingila ta maki kusan 10, wanda babu wanda ya taba kawo haka a ran sa.

A shekarar nan ne Hukumar FIFA ta ba Kocin na Leicester City kyauta a matsayin gwani-na-gwanaye cikin masu horaswa. Sai dai ga shi bayan wata guda an tsige Kocin bayan Kungiyar ta gaza tabuka wani abin kirki wannan shekarar.

KU KARANTA: Valencia ta ba Real Madrid mamaki

Abin mamaki ya faru a Duniyar kwallon kafa
Leicester ta kori Kocin ta

Kusan dai shekaru 4 da suka wuce duk Kocin da ya ci kofin Firimiya sai da ya bar Kulob din sa, fara daga Kocin Mancehester City Roberto Mancini, da na Manchester United Sir Alex Ferguson. Ga kuma Manuel Pellegrini na Man City, haka kuma Jose Mourinho ya bar Chelsea bara bayan ya ci Firimiyar wancan shekarar.

Wasu dai na ganin bai dace a sallami Claudio Ranieri ba komai ya faru, don kuwa a zaman Kulob din na shekaru 100 babu wanda ya taba irin kokarin sa. Sai dai kuma fa Kungiyar na cikin hadari babba. Manyan ‘Yan wasan ta Riyadh Mehraz da Jamie Vardy duk sun yi sanyi.

A same mu a http://twitter.com/naijcomhausa ko kuma a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel