Mufti Menk ya goyi bayan Sarkin Kano game da hana yawan karin aure
– Babban Malamin Duniya Mufti Menk ya goyi bayan Sarki Sanusi II
– Sarkin Kano yace za a hana talaka yawan aure a kasar sa
– Malamin yace Sarkin Kano yayi daidai kuma ‘Yan Jarida ba su kyautawa
Babban malamin Duniya mai fatawa Sheikh Ismail Menk ya goyi bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a game da maganar cewa za a hana talaka tubus kara auren mata a kasar sa. Kalamai da kudirin na Sarkin Kano sun jawo ce-ce-ku-ce a Gari.
Mufti Menk ya nuna goyon bayan sa ga yunkurin Sarkin yace dama can aikin Hukuma ne ta duba yadda ake gudanar da al’umarra ta kuma kawo gyara. Malamin yace ‘Yan Jarida ne ke kara hura wutar maganar inda suke nuna cewa Sarkin na nema yayi fada da Sunnar Manzon Allah SAW.
KU KARANTA: Buhari ya sha addu'o'i a Kano
Babban Shehin na kasar Zimbabwe yace ko da cewa aure Sunnah ne mai karfi, amma ko Manzon Allah SAW cewa yayi wanda yake da hali yayi, wanda kuma ba sa da shi sai ya hakura, ina kuma maganar karawa.
Malamin yace hakan zai kawo gyara a harkar aure inda za a mutunta darajar ‘ya ‘ya da kuma mata. A wata hira da Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN tayi da wasu mata a Maiduguri, wasu sun bayyana cewa hakan abu ne mai kyau yayin da wasu suka yi tir da batun.
Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng