Duk wanda ya ce na nemi shugabancin kasa yanzu ya na da tabuwan hankali – Kashim Shettima

Duk wanda ya ce na nemi shugabancin kasa yanzu ya na da tabuwan hankali – Kashim Shettima

Sakamakon ikirarin da Danlami Kubo, mataimakin kakakin majalisar dokoki na jihar Borno yayi a da farko, na shawaran cewa Shettima ne ya kamata ya shugabanci Najeriya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka mulki, gwamnan jihar Borno ya maida martani.

Duk wanda ya ce na nemi shugabancin kasa yanzu ya na da tabuwan hankali – Kashim Shettima

Gwamnan jihar Barno Kashim Shettima yace idan ba wai mutum yana da tabuwar hankali bane ta taya zai fara cewa wai wani ya nemi shugabancin kasa Najeriya yanzu da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake kokarin ganin ya samu lafiya tukuna.

Gwamna Shettima ya fadi hakanne da ya ke amsa bayanan da wani dan majalisar jiharsa mai suna Danlami Kubo yayi cewa wai shine yafi cancanta da ya zamo magajin Buhari idan ya gama wa’adinsa.

KU KARANTA KUMA: Yayinda Buhari ke waje, dan majalisa yayi yunkurin da Gwamna Shettima zai zamo shugaban kasa

Kashim Shettima yace maganganun dan majalisar yayi ta bata masa rai sannan kuma ya na sanar wa mutane cewa bashi da wata masaniya akan hakan.

Yace wannan magana da Danlami yayi ya yi matukar bata masa rai kuma yayi kokarin kiransa a waya domin samun tabbacin cewa shine ya fadi hakan ko kuma ba a rubuta abin da yace daidai ne ba.

Yace ba daidai bane ace wai shugaban kasa Muhammadu Buhari na can yana duba lafiyarsa wani kuma a nan yana kokarin kunno wutar da ba haka ba.

“Buhari shugaban kasa ne tsayayye, wanda kowa yayi na’am dashi, wanda ya kawo mana kusan karshen matsalar Boko Haram a yankin mu.

“Babu wani mai hankali da zai ce wai har ya fara nuna son kujeran shugabancin Najeriya bayan shugaban kasa ya na can ya na duba lafiyarsa.

“Menene yasa siyasa ke mai da wadansun mahaukata ne, mutum ya zamanto ba shi da tunani kwata-kwata.

” Wannan Magana ta dan majalisa Danalami ba magana ta bace kuma babu hannu na akai.

” Ina tare da Buhari, kuma idan zai yi takara a 2019 mune a gaba-gaba.” Inji Kashim Shettima

Asali: Legit.ng

Online view pixel