kaidodin jinin al'ada akan mata a addinin musulunci
- Haramun ne macen da take jinin al'ada ta yi azimi. Idan ta yi, bai zama Karɓaɓɓe ba. Amman za ta yi ramako azimin da ta sha lokacin al'adan
- Idan mace ta gama aikin hajji da umrah, sai ta ga al'adan ta kafin ta koma gida, kuma ya ci gaba har za ta baro hajji, za ta iya tafiya ba da ta yi ban kwanan tawaaf ba
Akwoi kaidodi da yawa akan al'ada da mata su ke a addinin musulunci. Sun fi ishirin, amma za mu lissafo wadana suka fi muhimmanci:
1. Sallah
Haramun ne mace ta yi sallah na farilla, ko kuma nafila lokacin da ta ke al'adan ta. Idan ta yi, bai zama Karɓaɓɓe ba. Bai zama wajibi ba ta yi wani sallah sai dai tana da tsarki, zalla ko kuma tsarki nda za ta iya duk rak’ah da ke cikin salla da za tayi.
2. Azumi
Haramun ne macen da ke al'ada ta yi azimi. Idan ta yi, bai zama Karɓaɓɓe ba. Amma, za ta yi ramakon azumin da ta sha lokacin al'adan.
3. kewaye dakin Allah
Haramun ne mace ta kaiwaya ka’bah tana al'ada ko wajibi ko kuma naafil. Idan ta yi kuma, bai zama Karɓaɓɓe ba. Dan manzon Allah (SAW) ya ce ma A’isha lokacin da ta ke al'ada cewar: “Ki yi komai da sauran masu hajji su ke, amma kar ki kewaye ka’bah sai ki na da tsarki.”
4. Tawaaf al-wadaa’ (ban kwana) bai zama mata wajibi ba
Idan mace ta gama aikin hajji da umrah, sai ta gan al'adan takafin ta koma gida, kuma ya ci gaba har za ta baro hajji, za ta iya tafiya ba da ta yi ban kwanan tawaaf ba.
5. zama cikin massallaci
KU KARANTA: Yadda wani tantirin Dan iska ya tuba ya musulunta
Haram ne mace da tana al'ada ta yi zama a cikin masalaci ko kuma filin Eid domin hadeeth ta Umm ‘Atiyyah (Allah ya mata albarka) ta ce ta ji manzo Allah (SAW) ya ce: “A bar yan matan da sun balaga, matan da baa bari su fita, da mata da suke alhada su je fili Eid.” Ama su tsaya a waje ba daga ciki ba.
6. Jima'i
Haram na mace ta yi jima’i a lokacin da ta ke al'ada, kar ta bar mijin ta ya yi jima’I da ita. Domin Allah yace: “Sun tambaye ka batun alhada. Ka ce: Adha ne, abin mai lahani, mai illa ne, miji ya yi jima’i da matar sa lokacin da ta ke al'ada, domin haka, a bar ta a lokacin sai ta na da tsarki, sai ta yi wanka.”
7. Mutuwan aure
Haram ne a kashe aure ma mace da ta ke al'ada.
8. Bukatan wanka (ghusl)
Idan mace ta gama al'ada, ya zama wajibi ta yi wanka, ta wanke duk jikin ta. Manzo Allah ya ce ma Faatimah bint Abu Hubaysh: “Idan al'adan ki ya zo, ki dena sallah, idan ya yanke, ki yi wanka ki soma salla.” A yadda al-Bukhaari ya fada.
Asali: Legit.ng