Muhimman abubuwa 4 da Ali Nuhu ya fada a gurin bikin Muhammad Bello

Muhimman abubuwa 4 da Ali Nuhu ya fada a gurin bikin Muhammad Bello

Ali Nuhu ya kasance babban jarumi kuma daraktan shirya fina-finai a kungiyar wasan hausa ta Kannywood. Ya kasance gwarzo wanda aka dama dashi kuma ake kan damawa dashi a harkar shirya fina-finan Hausa harma da na Kudu.

Muhimman abubuwa 4 da Ali Nuhu ya fada a gurin bikin Muhammad Bello

Gwarzon jarumi Ali Nuhu ya nuna farin cikin sa a gurin bikin auran abokin aikinsa Bello Muhammad Bello wanda aka gudanar a makon da ya gabata inda ya ke fadi wasu muhimman abubuwa tare dayi wa matasa nasiha kamar haka:

“Ina mutukar farin ciki da wannan biki da akayi Allah Ubangiji ya bada zaman lafiya tare da zuri’a dayyaba.”

KU KARANTA KUMA: Bani da wani abu da zaku gada – Buhari ga iyalansa

Ya kara da cewa: “hakika aure babban ni’ima ce da ba me gane ta sai wanda ya yita. Don haka matasa ina jawo hankalin ku da kuyi aure sannan kuyi biyayya ga iyayan ku dan ina da kyakkyawar zaton cewa biyayya ga iyaye shi ke iya sanadiyar zuwanka inda baka taba mafarkin zuwa ba.”

Ya kuma yaba kyawawan dabi’un angon inda yake cewa: “Bello Muhammad Bello ya kasance mutumin kirki ne, sannan kuma mutum ne me mutukar maida hankali a duk abun da yasa a gaba sannan yana da biyayya ga na kasa da shi har izuwa na sama da shi.”

A cewar sa B.M.B kamar yadda ake masa lakabi jarumine sosai bama a fina finai kawai ba a’a a duk inda yake, saboda duk mutumin dake son al’uma jarumi.

Daga karshe yayi ma ma’auratan addu’an samun zuri’a dayyiba da kuma fatan alkhairi a gidan aurensu.

Ku biyo mu: https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da nan https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel