Bani da wani abu da zaku gada – Buhari ga iyalansa

Bani da wani abu da zaku gada – Buhari ga iyalansa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace iyalansa ba za su gaji wani abun Kirki daga gareshi ba ko bayan bashi da rai.

Buhari ya ce ya shawarci ‘ya’yan sa da su zage su nemi ilimi domin shine kawai zai sa su iya rike kansu.

Buhari ya tabbatar da ganin cewa ‘ya’yan sa mata duk sunyi karatu har zuwa matakana jami’a.

Bani da wani abu da zaku gada – Buhari ga iyalansa

Wani Farsesa ne dan kasar Amurka ya fadi hakan a wata littafi da ya rubuta akan Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai suna “Muhammadu Buhari: “Gwagwarmayar shugabanci a Kasa Najeriya” wato “Muhammadu Buhari: The Challenges of Leadership in Nigeria,” a turance.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar musulman Shi’a sunyi sihiri a kan Buhari (HOTUNA)

Kamar yadda bayanai suka nuna akan kaddarorin da shugaba Buhari ya mallaka kuma ya mika wa hukumar kula da da’ar ma’aikata, Bayanai ya nuna cewa Buhari na da mallakin gidaje biyar ne kacal, Biyu a garin Daura, 1 a Kano, daya a Kaduna sannan da wadansu filaye biyu da bai gina su ba.

Bayan haka kuma yana da mallakin garken shanu, tumakai da awakai.

Haka kuma a bayanan da ya mika, Miliyan 30 ce kawai ya mallaka a asusun ajiyarsa dake bankin Union.

Buhari yana da motoci biyu da ya siya da kudinsa, banda wadanda aka bashi kyauta bayan harin da aka kai masa a Kaduna da kuma wadanda ya ke samu daga gwamnatin tarayya a matsayinsa na tsohon Shugaban kasa.

Ku biyo mu: https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da nan https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng