Sakon ranar haihuwa mai taba zuciya da Zahra Buhari ta aika ma Aisha Buhari

Sakon ranar haihuwa mai taba zuciya da Zahra Buhari ta aika ma Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasa Buhari kuma uwar jama’an Najeriya, Hajiya Aisha Buhari tana murnar zagayowar ranar haihuwarta karo na 46 a yau, 17 ga watan Fabrairu.

Sakon ranar haihuwa mai taba zuciya da Zahra Buhari ta aika ma Aisha Buhari
Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari

KU KARANTA KUMA: Kyawawan hotuna 6 na dan biloniya Ahmed Indimi da matarsa Zahra Buhari

Daya daga cikin ‘yayan Aisha Buhari wacce ta kasance farko gurin taya mahaifiyarta murna a shafin Instagram tare da sakon ranar haihuwa mai taba zuciya.

Sakon ranar haihuwa mai taba zuciya da Zahra Buhari ta aika ma Aisha Buhari

Tace: “Barka da zagayowar ranar haihuwa ga Uwargidan Najeriya Aisha Buhari. Amma mafi muhimmanci, barka da zagayowar ranar haihuwa gareki Mahaifiyata, haikalin girma,tafkin dubawa kuma haske ga duk mutumin da ya kusance ki.”

Sakon ranar haihuwa mai taba zuciya da Zahra Buhari ta aika ma Aisha Buhari

KU KARANTA KUMA: Uwa ta bayyana dalilin da yasa ta kashe jaririn ta

Kina da zuciyar tausayi, hikima sannan kuma ke dabance ta ko wace hanya. Allah ya daukaka ki ta ko wacce hanya ya ke mahaifiyata. Dubbin soyayya gareki.”

Soyayya dake tsakanin uwa da ‘yayanta yana da girma kuma babu abunda zai iya karya ta sannan kuma Zahra ta tabbatar cewa duk da tayi aure ga Ahmed Indimi, har yanzu iya yar mama ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel