Makashin maza: Ga Aisha dodon ‘Yan Boko Haram
– Aisha Gombi mai kamar maza tayi kaurin suna wajen fada da Boko Haram
– Ga wata jarumar mace mai yaki da ta'addan ‘Yan Boko Haram
– Aisha tace ‘Yan Boko Haram tsoron ta su ke
Jaridar Guardian ta dauko wani rahoto a game da wata mace mai kamar maza. Aisha Gombi dai mafarauciyar barewa ce a da, yanzu kuwa ta rikide farautar mayakan Kungiyar Boko Haram, kuma tayi kaurin suna don kuwa sun san ta. Aisha tana da shekaru 38 a Duniya.
Kwanaki da ‘Yan Boko Haram suka sace wasu yara ai sai kawai sai Sojoji suka dankarawa Aisha waya. Nan take ta shirya mafarauta aka shiga Dajin Sambisa. Dama can a kusa da dajin sambisa aka haifi Aisha Gombi Bakari ta kuma saba fita farautar manyan dabbobi tare da kakan ta.
KU KARANTA: An kama dan ta'addan Duniya a Najeriya
Aisha tace su kan su ‘Yan Boko Haram suna shakkar ta don kuwa ta saba kubutar da mutane daga hannun su. Aisha tana da bataliya inda ta ke jagorantar kattin maza wajen kubuto da wadanda ke hannun ‘Yan Boko Haram. Ba mamaki tana cikin wadanda aka dauka aikin soji a bara.
A Kudancin Kasar kuwa mun samu labari cewa an sace wasu baki ‘Yan kasar waje a cikin Kasar. Wannan abin kunya dai ya faru ne a Yamkin Neja-Delta mai arzikin mai a kasar.
A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook
https://www.facebook.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng