Kalli yadda wani Kasurgumin Kada ya hadiye Jakin dawa!
- Allah abin tsoro! dubi yadda wani kasurgumin kada ya hadiye wani jakin dawa.
- Wanna abin mamaki da ban tsoro ya faru ne gandun namun daji a kasar Kenya
Wannan lamari mai ban mamaki da ban tsoro ya faru ne a wani a gandun namun daji da ake kira Maasai Mara a kasar Kenya.
Wannan lamari dai ya faru ne a idon wani mai daukar hoton namun dawa ne mai suna Subramania Sridhan a inda shi kuma ya yi ta maza ya dauki hoton duk da hadarin yin hakan.
Na san ba kowa ne zai iya tsayawa kallon wannan al'amari ba, ko a hotunan bidiyo ne ko kuma na kati, amma ga Subramania Sridhan mai daukar hoto wannan ba komai ba ne musamman idan ka na juriya da kokarin ganin kwakwaf!!
Gani dai ya kori ji, ga hotunan
Tirakashi! lallai kam Ikon Allah sai kallo
Asali: Legit.ng