Wata Amarya ta rasu bayan daurin auren ta

Wata Amarya ta rasu bayan daurin auren ta

– Wata Amarya ta rasu makonni uku bayan an daure mata aure

– Amaryar ta rasu tana da juna biyu

– Asali ma dai ta rasu ne bayan ta haihu

Wata Amarya ta rasu bayan daurin auren ta
Wata Amarya ta rasu bayan daurin auren ta

Wani abin tausayi ya faru kamar yadda muka karanto a shafin Facebook. Wata Amarya dai tace ga garin ku nan, duka-duka ba ayi wata guda da yin auren ta ba. Wannan Amarya dai ta rasu jim kadan bayan an daura auren ta.

Wata kawar Amaryar mai suna Princess Nkiru ce ta bayyana haka yayin da ta ke mata ta’aziya a shafin ta na Facebook. Nkiru Momah tace dama can Amaryar tana da juna biyu, sai ga shi ta cika wajen haihuwar ‘da.

KU KARANTA: Wata 'Yar Najeriya na kwance a Asibitin Turai ba kudi

Kawar Marigayiyar tana mai kokawa da jimami da ce: ‘Dama na kwarai ba su dadewa.’ Har yanzu dai tana jin abin kamar a mafarki. An daura auren wannan Budurwa mai shekaru 23 a Watan Disamba, ta kuma haihu a Ranar 11 ga Watan Junairu, sai dai jim kadan bayan nan ta ce ga garin ku nan.

A wata Duniyar kuma Wani Soja mai suna Sulaiman Olamilekan ya kusa kashe wata Budurwa mai suna Jewel Infinity da duka a yayin da Budurwar ta ke kan hanyar ta na zuwa Garin Onisha. Yanzu haka dai wannan Budurwa tana Asibiti.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel