An rufe kantin shoprite a Kano kan haraji

An rufe kantin shoprite a Kano kan haraji

- An rufe kataferen kantin shoprite a Kano da rukunin kantunan da ke wurin a bisa kin biyan haraji

- Karamar hukumar birni da kewaye na bin hukumar kantin Naira miliyan 6 na wanda ta gza biya har na tsawon shekara biyu

An rufe kantin shoprite a Kano kan haraji
An rufe kantin shoprite a Kano kan haraji

An rufe kataferren kantin zamani na shoprite da ke kan titin zuwa gidan Zoo da ke kwaryar birnin Kano.

A wani rahoto da gidan Radio Rahma ya bayar a safiyar ranar Laraba 1 ga watan Fabarairu shekarar 2017 ya ce, an rufe rukunin kantunan na zamani na Ado Bayero Mall ne da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar.

A cewar gidan rediyon an rufe rukunin katunanan ne a bisa umarnin karamar hukumar birni da kewaye a bisa gaza biyan kudin haraji na naira milyan 6 har na tsawon shakra biyu.

An dai ga jami'an tsaro kofar harabar rukunin kantunan wanda ke karkame sun kuma hana kowa shiga yayin da ma'aikata su ka yi cincirindo a waje.

Ku biyo mu a shafinmm na Facebook a http://www.facebook.com/naijcomhausa ko a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa don karin bayani

Asali: Legit.ng

Online view pixel