Lebura yayi ma matar Malam ciki

Lebura yayi ma matar Malam ciki

Wani malamin Jami’a jihar Legas mai suna Suraju Oyekunle na cikin tsaka mai wuya irin na rayuwar aure bayan matarsa da suka shafe shekaru 13 ta yi cikin shege.

Lebura yayi ma matar Malam ciki
Malamin Jami'a Suraj Oyekunle

Jaridar P.M Express ta ruwaito cewar matar malamin mai suna Kafayat ta amsa laifin kebewa da wani Lebura mai suna Fatai Alimi wanda a cewar ta shine ya dibga mata cikin, bugu da kari Uwargida Kafayat tace ita dai tafi kaunar Leburan ma akan Malamin jami’ar, don haka zata tattara inata inata ta koma auren Lebura.

Uwargida Kafayat mai shekaur 36 ta kwashe kayanta tas! daga dakin mijinta inda ta koma dakin Lebura Fatai Alimi duk a unguwar da suke zaune Igando, tun a watan Oktoba lokacin da mijinta yayi wani balaguro.

KU KARANTA: Fasto dan luwadi ya bayyana matar shi namiji yana da ciki

Lebura yayi ma matar Malam ciki
Kafayat da Lebura Alimi

Ita dai Kafayat ta bayyana cewar tafi samun kwanciyar hankali a dan tsukukun dakin Leburan fiye da gidan alfarma irin na mijinta. Sa’annan harda yaronta mai shekaru 12 ta tattara zuwa gidan Lebura Fatai Alimi.

Sai dai a ranar Alhamis 10 ga watan Nuwamba ne yansanda suka kama Fatai Alimi bayan mijin Kafayat ya kai karar su ofishin yansanda. Ko a nan ma dai Kafayat ta nuna ma Lebura kauna inda ta biya N25,000 kudin belinsa.

Daga nan sai ta kara da cewar ta rabu da mijinta ne sakamakon sun kasa samun haihuwa har na tsawon shekaru 13, kuma ta koka kan yarda mijin nata ke gaza nuna mata kulawa yadda ya dace. Uwargida Kafayat tace amma daga haduwar tad a sabon saurayinta hart a samu juna biyu, kuma suna zamansu cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel