Dalilin da yasa na zagi shugaba Buhari, Sanata Shehu Sani yayi magana
Sanata Shehu Sani dake wakiltan Kaduna ta tsakiya ya karyata rahotannin cewa jam’iyyarsa ta mai ci, All Progressives Congress (APC) ta gayyace shi kan furucinsa game da wasikar shugaban kasa Buhari zuwa majalisar dattawa.
Sani ya buga wani dan takaitaccen jawabi a shafinsa na zumunta a Facebook da Tuwita a daren ranar Juma’a, 27 ga watan Janairu inda ya karyata rahotannin cewa jam’iyyar APC ta aika sammaci a gare shi.
Ya tabbatar wa dubunan mabiyansa a shafukan biyu cewa zai sanar da su idan APC ta gayyace shi.
KU KARANTA KUMA: APC ta sammaci Shehu Sani kan harin baki da ya kaiwa Buhari
Ya rubuta: “Ban samu ko wani “takardan gayyata ko sammaci ba” daga hedkwatar APC ta kasa ba kamar yadda kafofin watsa labarai suka rahoto.
“Idan irin haka ta faru tabbass zan amsa gayyata kuma zaku samu labarin haka ta shafukana na Tuwita da Facebook.”
Har ila yau Sani yayi bayani a wani dan takaitaccen rubutu a Tuwita kan dalilin da yasa ya zagi shugaban kasa Buhari.
Ku tuna cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana yaki da rashawan shugaban kasa Buhari a matsayin san kai.
Da yake magana a gaban majalisa a ranar Talata, 24 ga watan Janairu, Sani ya karyata wasikar da shugaban kasa ya aika wa majalisa wanda ya wanke babban sakataren gwamnatin tarayya David Lawal daga aikata zargin cin hanci da kwamitin majalisa ke zargin sa a kai.
Asali: Legit.ng