LABARI DA DUMI-DUMI: ‘Yan Shi’a da dama sun samu rauni

LABARI DA DUMI-DUMI: ‘Yan Shi’a da dama sun samu rauni

– ‘Yan Shi’a sun fafata da Jami’an tsaro a Abuja; da dama sun jikkata

– Kungiyar ‘Yan Shi’a na zanga-zanga domin a saki Zakzaky

– Ibrahim El-Zakzaky dai ya dade a hannun Hukuma a daure

LABARI DA DUMI-DUMI: ‘Yan Shi’a da dama sun samu rauni
LABARI DA DUMI-DUMI: ‘Yan Shi’a da dama sun samu rauni

Kamar yadda muka kawo rahotanni a baya. Wasu daga cikin ‘Yan Kungiyar IMN ta Shi’a sun gwabza da Jami’an tsaro na ‘Yan Sanda a Garin Abuja inda ‘Yan Kungiyar ke zan-zanga nema a saki Malamin su, Ibrahim Zakzaky.

‘Yan Kungiyar dai sun yi zanga-zanga ne har a gaban Majalisar Tarayya, sai dai kuwa sun sha barkonan tsohuwa daga Jami’an ‘Yan Sanda. ‘Yan Kungiyar dai suna nema ne a saki Malamin su da Matar sa wanda sun fi shekara guda a tsare.

KU KARANTA: Yan Shi'a sun yi bikin Kirismeti

Alkali Gabriel Kolawaole ya bada umarnin a saki Zakzaky da gaggawa. Sai dai har yanzu Gwamnati tayi mursisi tana cigaba da rike Shugaban na Shi’a. Jama’a da dama ne dai suka jikkata a wajen zanga-zangar.

Kwanan nan kuma Kungiyar NUJ ta ‘Yan Jaridun Najeriya ta soke rajistar Jaridar nan ta Al-Mizan. Kungiyar ta bayyana cewa ta gano Jaridar Jaridar Al-Mizan din da kuma ta Turancin ta watau Pointer Express ta Kungiyar IMN ce ta ‘Yan Shi’a.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng