Abin mamaki: Akuya da kwankwadar lemun kwalba (Bidiyo)
Kamar dai yadda Hausawa ke cewa, inda ranka ka sha kallo! A nan kuma an samu wani faifan bidiyo na ban mamaki ne dake yawo a shafukan sadarwa na yanar gizo na wata Akuya mai basira.
Ita wannan Akuyar dai an nuna ta ne tana shan lemun kwalba bayan ta daga kwalban sama sai ta zuke lemun dake cikin kwalbar, jama’a kwalba fa!
KU KARANTA: Labarin wani mutum mai nauyin kilo 435, yana kalaci da ƙwai 36, nama kilo 3 da madara lita 5
Wannan farar dabara ta Akuyar ya sanya jama’a kyalkyacewa da dariya sakamakon ba kowanni dabba bane zai iya aikata hakan.
A takaice dai wannan Akuyar na shan lemun kwalba ne kwatankwacin yadda mutane ke shan lemu daga kwalba. Ga dai yadda bidiyon Akuyar yake.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http:/twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng