Karambani: Yaro yayi ma kansa ‘kaciya’ da takobi
Wani karamin yaro wanda ko Akuya bata kais hi karambani ba ya ji wa kansa mummunar ciwo yayin da yayi kokarin yi ma kansa kaciya wai don abokansa suna masa gori.
Shidai karamin yaron ya aikata wannan aika aika ne bayan abokansa sun bayyana masa cewar ba zai taba samun budurwa ba muddin ba shi da kaciya.
Bayan faruwar lamarin ne sai yaron ya shiga wani mummunan hali, inda da kyar aka kwace rayuwarsa bayan an garzaya dashi asibiti akan lokaci, a can aka barshi yayi jinyar kwanaki biyu kafin daga bisa ak sallamo shi.
KU KARANTA:Hukumar INEC ta dirza ma’aikatanta 200 akan cin hancin N23billion
Wani daga likitocin asibitin George Mature yace lamarin yaron yazo da sauki, saboda naman wajen mazakutar tasa kawai ya yanke. Likitan yace:
Lamarin yaron da sauki, tunda fatar waje ya yanke, don haka ne muka kwantar da shi don bashi kulawa sakamakon gudun kada cututtuka su shiga cikin ciwon.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijhausacom ko http://twitter.com/naijhausacom
Asali: Legit.ng