Dangote ya kafa kamfanin kera manyan motocin daukan kaya a Najeriya

Dangote ya kafa kamfanin kera manyan motocin daukan kaya a Najeriya

Shahararren dan kasuwannan kuma wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika Aliko Dangote ya kafa wata sabuwar kamfanin kera manyan Motoci a kasa Najeriya.

Dangote ya kafa kamfanin kera manyan motocin daukan kaya a Najeriya
Alhaji Aliko Dangote
Asali: Facebook

An kafa kamfanin ne a jihar Legas.Dangote yace kamfanin zata dinga kera akalla manyan motoci 10,000 duk shekara.

KU KARANTA KUMA: Mustapha Indimi yayi wa matarsa Fatima Sheriff wankan naira dubu-dubu a gurin bikinsu

Wani mai Magana da yawun kamfanin, ya sanar da cewa kamfanin sun hada hannu ne da wata kamfanin kera motoci dake kasar China domin samun nasara akan hakan.

Dangote na shirin kaddamar da sabuwar kamfanin matatar man sa da na yin takin zamani a shekara ta 2017.

Daga karshe yace dole ne a hana karfi da karfe domin ganin an kafa kamfanoni a kasa Najeriya domi samun kudaden shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng