Wata mata ta haifi da namiji a cikin motan BRT a Lagas (hotuna)

Wata mata ta haifi da namiji a cikin motan BRT a Lagas (hotuna)

Hakika Allah buwayi mai ne mai banmamaki!

A ranar Laraba, 11 ga watan Janairu, an rahoto cewa wata mata mai dan shekaru ta haifi da namiji a cikin motan BRT.

Wata mata ta haifi da namiji a cikin motan BRT a Lagas (hotuna)
Wata mata ta haifi da namiji a cikin motan BRT a Lagas

A cewar wadanda abun ya afku a idannunsu, sun bayyana cewa matar ta haihu da misalin karfe 9 na safe a hanyar Ketu/Mile 12, Lagas. Sun kara da cewa, ta yi hayan mota zuwa tashar Irawo, zata asibitin dake Iyanapaja amma lokacin haihuwar ta yayi yaron ya kasa jira.

KU KARANTA KUMA: An kama mahaukaci yana kokarin sace yara biyu a Delta (hotuna)

Da zaran lokacin da ta shiga mota, ta kasa samun kwanciyar hankali kuma ta fara fita hayyacinta a take sauran pasinjoji mata suka hada hannu suka taimaka mata ta haifi yaron, yayinda suka lullube jaririn da kaya.

Other passengers were transferred into another bus as the woman was then taken to the hospital

Allah ya raya!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng