Al’amura sun daidaita a garin Baga ta jihar Borno
- Al’amura sun daidaita a garin Baga ta jihar Borno wacce Boko Haram suka tarwatsa a shekarar 2015
- A shakarar 2015 Kungiyar Amnesty International ta zargi Boko Haram da kisan kiyashi a garin wanda ya ja hankalin duniya, amma rundunar sojin Najeriya ta musanta
Rahotanni na nuna cewa komai ya daidaita a garin Baga da ke jihar Borno.
A wasu jerin hotuna da wani mazaunin garin mai suna Baba Bala Meleh ya dauka, kuma Jaridar Rariya ta wallafa a dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook a ranar 11 ga watan Janairu shekara 2017, hotunan sun nuna yadda jama’a ke hada-hadarsu ta yau da kullum a garin.
Garin na Baga na daya daga cikin garuruwan da Boko Haram ta mamaye ta kuma tarwatsa jama’ar garin tare da tilasta musu gudun hijira.
A wani rahoto da kungiyar Amnesty International ta fitar a shekarar 2015, ta ce Boko Haram ta yi barnar da ba a taba ganinta ba a tarihin fadace-fadacen ‘yan ta da kayar baya, a inda Boko Haram a lokaci guda ta hallaka mutane 2,000.
Sai dai a wani martani da rundunar sojin Najeriya ta bayar tdangane da rahoton, mai magana da yawon shalkwatar tsaro ta waccen lokacin, Manjo Janar Olukolade ya musanta rahoton tare da cewa mutanen da suka hallaka 150 ne, ciki har da ‘yan ta’addan.
Sai dai wasu majoyoyi na cewa, ‘yan Boko Haram a waccan lokacin sun ragargaza akalla garuruwa 16 na jihar a wasu jerin hare-hare da Boko Haram ta kai mutane 2,000 suka mutu ciki har da wadanda suka hallaka a tafkin Chadi a kokarinsu na tsira da rayukansu.
Ku cigaba da bin mu a shafin mu na Facebook a https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da kuma a Tuwita a https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng