An fitar da sunayen wadanda za suyi jigilar mai a shekarar 2017

An fitar da sunayen wadanda za suyi jigilar mai a shekarar 2017

– Kamfanin NNPC na Kasa tace Kamfuna 39 aka ba damar shigo da mai

– A ciki akwai Kamfanun Najeriya da kuma Kasashen waje

– NNPC tana shirin kara gyara Masana’antu tatar man Kasar

An fitar da sunayen wadanda za suyi jigilar mai a shekarar 2017
An fitar da sunayen wadanda za suyi jigilar mai a shekarar 2017

Kamfanin main a Kasa watau NNPC ya fitar da jeringiyar sunayen Kamfunan da aka ba damar shigo da mai cikin Kasar nan wannan shekarar. A ciki akwai Kamfunan ‘Yan Kasuwar Najeriya guda 11 da na Kasar Turai 3 da kuma Kamfunan Kasa watau NOC da wasu da ke karkashin NNPC din.

Masana’antu da za su yi aiki sun hada da Hindustan da Varo da kuma Sonara da Cepsa da Bharat. Sannan kuma akwai ‘Yan kasuwan Kasa da Kasa irin su BP Trading, Heritage Oil da sautan su. Gwamantin Kasar India da kuma Kasar China suna cikin jerin.

KU KARANTA: Harin bama a Ebonyi?

Kamfunan Najeriya da aka ba dama sun hada na AA Rano, Oando, Sahara Energy da dai sauran su. Kwanan nan za a fara gyaran Matatatun man Kasar inji wani Babban Jami’in Hukumar da ke Abuja, hakan zai kawo gyara a sha’anin harkar man Kasar.

Kwanaki Hukumar ta karyata rade-radin samun canzi a farashin man fetur din Kasar. NNPC tace tana da tsarin da zai cigaba da samar da man fetur ga Kasar har na wani dogon lokaci, wanda hakan ba zai bada damar a taba kudin ba.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng