An yi sauye-sauye a Gidan Kwastam
– Kwastam tayi wasu ‘yan sauyi a Gidan na ta
– Shugaban Kwastam din na kokarin shiryawa sabuwar shekara
– Motoci kuma dai na nan a Kasa, an gagara shigo da su
Shugaban Kwastam na Kasa, Kanal Hammed Ali mai ritaya ya amince da wasu ‘yan sauye-sauye da aka yi a Gidan domin shiryawa sabuwar shekarar nan da kyau. Sauyin da aka yi dai za su taimaka wajen karawa Hukumar karfi kamar yadda aka fada.
An dai canzawa Manyan Ma’aikata da dama wajen aiki, wannan mataki kuma zai fara aiki ne ba tare da wani bata lokaci ba. Gidan Talabijin na Kasa watau NTA ta kawo wannan labara. A cikin wadanda abin ya shafa akwai wasu manya har guda 46.
KU KARANTA: An tsige Shugaban Majalisa
Cikin Wadanda abin ya shafa akwai mataimakan Shugaban Kwastam din watau masu matsayin ACG har guda 8. Sun hada da: Abdulkadir Azerema, Umar Sanusi, Mondau Abueh, Augustine Chidi, Charles Edike, Aminu Dangaladima. Ahmed Muhammad, da kuma Francis Dosunmo.
Hukumar kuma ta kara tabbatar da haramcin shigo da motoci ta Kasa. Yanzu haka dai akwai motoci makil da ba a gama aikin karaso da su cikin gari ba a bakin iyakokin Kasar. A bayan nan ne Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bada umarnin hana shigo da motoci fadin Kasar nan ta iyakar Kasa. Gwamnatin Kasar dai tace haramcin ya shafi sababbi da tsofaffin motoci zuwa cikin Kasar ta Najeriya.
Asali: Legit.ng