Kyawawan hotuna daga kasaitaccen auran yar gwamnan jihar Sakkwato

Kyawawan hotuna daga kasaitaccen auran yar gwamnan jihar Sakkwato

- Yar gwamnan jihar Sakkwato Aisha ta yi aure da angonta Muhammad Dikko Dahiru, kasaitaccen biki da akayi a gidan gwamnatin jihar Sakkwato

- Daurin auran ya samu halartan manyan masu fada aji a Najeriya wadanda suka hada da shugaban kasa Buhari

Kyawawan hotuna daga kasaitaccen auran yar gwamnan jihar Sakkwato
Aisha da kawayenta

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da sauran yan uwansa suna murnar shiga sabon shekara kamar yadda daya daga cikin yayansu Aisha ta daura aure da angonta Muhammad Dahiru Dikko a yau.

KU KARANTA KUMA: Kyakkyawan sauyi na nan tafi a 2017 inji Shugaba Buhari

Anyi hadadden kamu irin na al’addan Bahaushe da yan arewa a daren jiya a gidan gwamnati.

Ga wasu daga cikin hotunan bikin:

Kyawawan hotuna daga kasaitaccen auran yar gwamnan jihar Sakkwato
Kawayen Aisha
Kyawawan hotuna daga kasaitaccen auran yar gwamnan jihar Sakkwato
Aisha da kawayenta na rawa

Bikin ya ci gaba tare da manyan masu fada a aji a Najeriya sun halarci taron bikin. Wadanda suka hada da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai Dogara da shugaban kasa Buhari wanda ministan shari’a, Alhaji Abubakar Malami ya wakilce shi. Kalli a kasa:

Kyawawan hotuna daga kasaitaccen auran yar gwamnan jihar Sakkwato
Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara tare da ma'auratan
Kyawawan hotuna daga kasaitaccen auran yar gwamnan jihar Sakkwato
Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da matarsa, shugaban majalisar dattawa, Saraki, sababbin ma’auratan, kakakin majalisa Yakubu Dogara, Alhaji da Misis, Dahiru Mangal, a gurin biki

An bayar da auran amaryar ga Dikko, dan attajirin dan kasuwa mazaunin Katsina, Alhaji Dahiru Mangal bayan an biya sadaki na naira dubu dari daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel