Kwallon kafa: Ko kun san nawa wanda yafi kowa albashi yake dauka duk sati?
Tsohon dan wasan gaba na Manchester City da Man United Carlos Tevez ya zama dan kwallon da ya fi daukar albashi a duniya, da fan dubu 310, kwatankwacin naira miliyan 186 a sati, bayan ya koma Shenhua ta China.
Shanghai ta dauki dan wasan na gaba dan Argentina mai shekara 32, daga kungiyar Boca Juniors, amma babu wani cikakken bayani da aka bayar kan yarjejeniyar, amma an ce kwantiragin na shekara 2 ne.
Sai dai wasu rahotanni sun ce Shanghai wadda tsohon kocin Brighton Gus Poyet ya koyar, ta amince da kwantiragin a kan kusan fan miliyan 40 tare da biyan dan wasan albashin fan 310,000, kwatankwacin naira miliyan 186 a sati.
Tevez ya yi wasa a gasar Premier tsawon shekara bakwai, kuma ya dauki kofuna da kungiyoyin Manchester biyu, City da United
Haka kuma ya dauki Kofin Zakarun Turai da United a 2008, kafin ya koma Juventus a 2013, inda ya ci kofuna biyu a Italiya.
Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa
Ku biyo a shafin fezbuk: Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng