Ba maraya sai rago: Kalli yadda guragu ke neman kudi
Wasu guragu su biyu sun tabbatar da wannan maganar da ake cewa ba maraya sai rago.
An hangi guragun su biyu ne suna share wata gadar sama a garin Abuja, don samun abun sakawa a bakin salati.
Mun samu labarin nan ne daga wani ma’abocin kafar sadarwa ta Facebook mai suna Kabaka Oladimeji Adekanbi, ga yadda ya bada labarin:
KU KARANTA:Ko ka san hamshakin Attajirin daya dauki nauyin dawainiyar yan matan Chibok?
“A kullum idan naga guragun nan su biyu, ina kara samun kwarin gwiwa tare da kishin kasa ta Najeriya, wani zubin sai in dinga mamakin yadda basa gajiyawa wajen sharan gadar Lugbe wanda mutane masu karfi da lafiya ke batawa.”
Da wannan nake ganin ya kamata mu baiwa kawunan mu amsar wannan tambaya, ‘me zamu yi ma kasar mu?’
Ku cigaba da bibiyan labaran mu a nan ko a nan.
Asali: Legit.ng