Kalli cikin katafaren gidan Dangote dake Abuja (Hotuna)

Kalli cikin katafaren gidan Dangote dake Abuja (Hotuna)

Hotunan cikin gidan mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya karade yanar gizo.

Katafaren gidan miliyoyin dala dake Abuja ya kai kimanin dala miliyan 30 (naira biliyan 5) cike yake da kayan alatu. Dangote ya kira katafaren gidan tsawon shekaru goma sha biyu, kuma kwanan nan ya kammala sabon estate a kasar Amurka.

Kalli cikin katafaren gidan Dangote dake Abuja (Hotuna)
Mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote
Asali: Facebook

Da yake Magana game da palon shakatawarsa, yace:

“Talbijin abune da ke nishadantar da kai a falon ka saboda idan babu mutane a gida. Ina son kallon talbijin. Ina kallon tashoshin kasuwanci sosai, kamar su Bloomberg TV, wanda shi nafi so a cikin tashoshi da dama. Ina duba zuwa ga ranar da Afrika zata samu ingantacen kafofin watsa labarai, wanda zai nishadantar damu sosai. Amma kwarai, sannu da zuwa, wannan shine palo na.

Kalli cikin katafaren gidan Dangote dake Abuja (Hotuna)
Nan ne gurin da Dangote ya ke tarban manyan yansuwa da jami'an gwamnati

Da yake Magana game da kitchen dinsa, yace: “An ce kitchen ya kasance zuciyar gida. Guri ne da ake girka abinci- shi ke gina jiji, zuciya da ruhi na yan’uwa da abokan arziki a fadin duniya. Wasu sun ce yayinda aka samar da rayuwa a daki, amma a kitchen yake rayuwa.”

Kalli cikin katafaren gidan Dangote dake Abuja (Hotuna)
Kitchen

Da yake Magana game da ofishin gida, mai kudin Afrika yace: “Imma kana aiki gaba daya a gida ko kuma kana yin wasu yan sa’aoi a sati, shirya ofishin ka na gida yana da mutukar muhimmanci don kwanciyar hankalinka da himma. Na tarbi mutane masu muhimmanci da dama a nan, wadanda suka hada da Bill Gates, shugaban kasa Goodluck Jonathan, da wasu da dama da ban ambata ba.

Kalli cikin katafaren gidan Dangote dake Abuja (Hotuna)
Ofishin gida

Game da dakin kwanan sa, Dangote yace:

“Ban ji dadi ba nuna maku inda nake kwana, kun sani. Amma ga inda nake kwana. Ni da matata muna iya kokarinmu don ganin mun gyara gurin sosai. Na fada maku gaskiya, bana kashe lokuta sosai a nan kamar ofishi na da duk wani guri da nake aiki. Ina daukar hutu da muhimmanci kuma na karanta labaru da bincike da dama da ya nuna muhimmancin bacci na akalla awanni takwas. Amma mai zai sa mutun yayi bacci da yawa? Don hutu? Kar ku kasa fahimta na, hutu na da kyau, amma idan kana son yin bacci, talauci zai zama rabonka. Don haka ga dakin baccina, mu ci gaba."

Kalli cikin katafaren gidan Dangote dake Abuja (Hotuna)
Dakin kwana

Asali: Legit.ng

Online view pixel