Jay-Jay Okocha yayi bayani

Jay-Jay Okocha yayi bayani

– Babban Dan wasan Najeriya Austin Jay Jay Okocha ya bayyana dalilin da ya say a ajiye kwallo yana matashi

– Jay Jay Okocha yace rashin taka leda da kyau ya sa ya bar kwallo

– Babban dan wasan ya bugawa su Bolton Wanderers daga shekarar 2002 har 2006

Jay-Jay Okocha yayi bayani
Jay-Jay Okocha yayi bayani

Babban dan wasan Kasar nan kuma tsohon Kyaftin ya bayyana babban dalilin da ya sa ya ajiye kwallo da wuri. Tsohon mai rike da kambun Super Eagles yace rashin buga wasanni a kai-a kai ya sa ya ajiye kwallon.

Dan wasan Duniyan Okocha wanda ake yi wa lakabi da Jay Jay ya ajiye kwallon kafa ne a shekarar 2008. Wannan abu ya ba kowa mamaki, domin kuwa babu wanda yayi tsammanin haka. A wancan lokaci Okocha yana da shekaru 34 ne a duniya.

KU KARANTA: Tsarin cacar MMM

Okocha yace bai ga amfanin ya horu tun daga Litinin zuwa Jumu’a ba, sai kuma ya buga wasa na minti 20 a cikin fili. Sannan kuma ya kara dawowa aiki washegari Lahadi. Okocha yace shi mutum ne mai son takara da bugawa da sauran Jama’a.

Okocha ya ajiyewa Najeriya kwallo ne a 2006. Kwanaki da aka tambayi tsohon Kocin Ingila, Sam Allardyce ko wani Kyaftin ne ba zai manta da shi ba, Kocin ya bada amsa da Okocha. “Idan dai kana neman Kyaftin a cikin fili da waje sai Okocha”, Inji Allardyce. “Yana jin yaruka dabam-dabam har hudu, ya iya turanci sosai, ya taimkawa ‘yan Kasar da ba su jin turanci…’ Inji Allardyce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng