Gwamna Ayade ya shirya nada sababbin mataimaka 6,000, da samar da ayyuka 50,000
- Gwamna Ben Ayade y ace zai nada babbabin mataimaka 6,000 kuma zai samar da ayyuka 50,000 daga watan Janairu na shekarar 2017.
- Ya ce nada sababbin mataimaka zai bunkasa gwamnati kuma zai ba mazauna jihar damar samun abinci a gidajensu
- Gwamnan na jihar Cross River ya sha alwashin tabbatar da cewa babu wanda baida aikin yi a jihar
A ranar Litinin, 19 ga watan Disamba, Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers yace zai nada sababbin mataimaka 6,000 kuma zai samar da ayyuka 50,000 daga watan Janairu na shekarar 2017, jaridar Punch ta ruwaito.
A cewarsa, nadin sababbin mataimaka zai bunkasa gwamnati kuma zai sa mazauna jihar su samu abinci, yayinda samar da ayyuka zai tabbatar da cewa babu wanda baida aikin yi.
Ayade ya bayyana haka a U.J. Esuene stadium a lokacin wani taro da akayi don girmamashi bayan babban kotu ta yanke hukunci a kansa a ranar 9 ga watan Disamba.
KU KARANTA KUMA: Mutane hudu sun mutu bayan karo tsakanin yan sanda da masu satan mutane
Gwamnan ya kuma sanar da bayar da kyautan naira miliyan 50 da naira miliyan 30 ga kungiyar Kiristocin Najeriya da kuma na al’umman musulmai a jihar.
Ku tuna cewa babban kotu ta kaddamar da Ben Ayade na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin gwamnan jihar Cross River.
Asali: Legit.ng