Bayan Boko Haram, Sabon tashin hankali ya kunno kai a Arewa-maso-Gabas

Bayan Boko Haram, Sabon tashin hankali ya kunno kai a Arewa-maso-Gabas

Rahotanni daga jihar Taraba a Najeriya na cewa akalla mutane 24 sun rasa rayukansu, yayinda da wasu dama suka bace, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin ‘yan kabilar Tibi da Fulani a kauyen dan Anacha.

Bayan Boko Haram, Sabon tashin hankali ya kunno kai a Arewa-maso-Gabas
Bayan Boko Haram, Sabon tashin hankali ya kunno kai a Arewa-maso-Gabas

Wata majiya daga jihar ta ce rikicin ya soma ne tun a jiya asabar, bayan da aka gano gawarwakin Fulani guda biyu da aka kasha yashe a jeji, wanda hakan yasa wasu daga ciki fara kai hari kan ‘yan kabilar Tibi da suke zargi.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar David Misal ya tabbatar da barkewar rikicin, inda ya ce an aike da jami’an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.

Sai dai har zuwa lokacin da muka wallafa wannan labari hukumar 'yan sandan jihar bata sanar da alkalumman wadanda suka rasa rayukansu ba a hukumance.

Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa

Ku biyo a shafin fezbuk: Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel