Buhari@74:abubuwa 6 game da Muhammadu Buhari da ya kamata ku sani

Buhari@74:abubuwa 6 game da Muhammadu Buhari da ya kamata ku sani

Kamar yadda shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya cika shekaru 74 a yau, Asabar 17 ga watan Disamba 2016. Nasarar da yayi a zaben 2015, ya kasance na farko a tarihin Najeriya shugaban kasa mai ci ya fadi zabe ga dan takarar jam’iyyar adawa a zaben shugabancin kasa.

Duk da kalubalan da ya fuskanta a lokacin mulkin soja, soyayyarsa ga kasar ya kuma basa daman shugabantar kasar a gwamnatin demokradiya.

Ya yinda yake murnar cika shekaru 74, ga abubuwa guda 6 da ya kamata ka sani game da shi.

1. Matsayinsa a ahlin gidansu

Buhari@74:abubuwa 6 game da Muhammadu Buhari da ya kamata ku sani
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana matashi

An haifi shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disamba, shekarar 1942, a Daura, jihar Katsina. Buhari ya kasance da na ashirin da uku (23rd) ga mahaifinsa Adamu.

Ya taso a hannun uwarsa Zulaihat kadai saboda mahaifinsa ya rasu yana dan yaro karami.

2. Tashin sa

Buhari@74:abubuwa 6 game da Muhammadu Buhari da ya kamata ku sani
Shugaba Muhammadu Buhari a halin samartaka

Mahaifinsa ya rasu lokacin yana da kimanin shekaru hudu a duniya. Buhari ya taso a hannun mahaifiyarsa Zulaihat tare da taimakon Mamman Daura da kuma yan uwansa. Ya halarci makarantar firamare a Daura da Mai’adua.

3. Aikinsa na soja

Buhari@74:abubuwa 6 game da Muhammadu Buhari da ya kamata ku sani
Muhammadu Buhari a matsayin jami'in soja

Ya shiga aikin soja yana da shekaru 19 a duniya, bayan yay i makarantar horon sojoji wato Nigerian Military Training College (NMTC) a 1961.

Kasancewar sa a cikin juyin mulkin soja na Disamba 1983, wanda ya sauke shugaban kasar demokradiya Shehu Shagari, Buhari yay i aiki a matsayin shugaban kasa a mulkin soja daga 1983 zuwa 1985.

4. Ka’idodin sa

Buhari@74:abubuwa 6 game da Muhammadu Buhari da ya kamata ku sani
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Buhari ya kasance mutun mai nuna gaskiya da kuma bin ka’idar kashe kudade, wannan ne yasa ya saka fifiko kan yaki da rashawa.

Tsakanin watanni 20 a matsayin shugaban kasa, an tura kimanin yan siyasa 500, jami’ai da kuma yan kasuwa gidan yari saboda rashawa. An saki wadanda aka tsaren bayan sun saki kudade ga gwamnati da kuma yarjejeniyar cike wasu ka’idodi.

5. Iyalansa

Buhari@74:abubuwa 6 game da Muhammadu Buhari da ya kamata ku sani
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Safinatu

Buhari ya auri matarsa ta farko, Safinatu yana da shekaru 29 a 1971. Safinatu ta kuma kasance matar shugaban kasar Najeriya daga Disamba 1983 zuwa Augusta 1985.

Sun haifi yaya biyar tare, mata hudu da namiji daya. Sun sanya wa yarsu ta fari, Zulaihat wato ta ci sunan mahaifiyar Buhari.

Bayan sun rabu da Safinatu a 1988, ya auri matarsa ta biyu kuma matarsa a yanzu Aisha Buhari a Disamba 1989.

Har ila yau sun samu yara biyar tare, namiji daya mata hudu. Sune Aisha, Halima, Yusuf, Zahra da kuma Amina.

6. Rashin sa

Buhari@74:abubuwa 6 game da Muhammadu Buhari da ya kamata ku sani
Shugaba Muhammadu Buhari

Buhari ya dandani zafin rashi tun yana dan yaro, idan kun tuna, ya rasa mahaifinsa yana da karancin shekaru, yayinda mahaifiyarsa ta rasu, yana cikin tsakanin karshen 40s.

Safinatu Buhari, matsarsa da suka rabu ta rasu bayan kamuwa da ciwon suga haka kuma yarsa ta farko, Zulaihat ta rasu sakamakon cutar sikila, jim kadan bayan ta haihu a Nuwamba 2012, a wani asibiti a Kaduna. Har ila yau ya rasa dansa Musa, daga aurensa na farko.

Duk da wannan dubin rashi da yayi a baya ya zamo mutun mafi karfi a Najeriya.

Muna taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng