Auren Zahra Buhari da Ahmed Indimi (yanda yake wakana)
Za’a daura auren (nikkai) da kowa ke jira na yar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra Buhari a yau, Juma’a 16 ga watan Disamba.
Auren Zahra ya yi tashe a kafofin watsa labarai yan makonni da suka wuce lokacin da aka sanar da dakatar da aurenta da dan miloniya Mohammed Indimi, Ahmed.
KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta ba da kyautan kayan abinci ga Kiristoci don bikin Kirsimeti
Kyakkyawa Zahra wacce ta fi kowa shahara a cikin yayan shugaban kasa da Ahmed Indimi sun fara gudanar da bikinsu a farkon wannan mako tare da wani liyafa mai kayatarwa sannan kuma akayi taron shan shayi.
A ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, Aisha Buhari tayi taron daren kunshi na musamman don masoyiyar yar tata, Zahra Buhari.
Asali: Legit.ng