Anci mutuncin wata budurwa dalilin Saurayinta

Anci mutuncin wata budurwa dalilin Saurayinta

Wata budurwa taci na jaki a wani shagon gyaran gashi dake kasar Zimbabwe bayan saurayinta da yayi alkawarin biyan kudin gyaran gashin ya tsere ya barta.

Anci mutuncin wata budurwa dalilin Saurayinta
wata mace

Lamarin dai ya faru ne a wani shagon gyaran gashi mai suna Rich and Famous Hair Salon dake kasar Zimbabwe, kuma rahotanni sun bayyana cewa budurwar mai suna Nathando taje gyaran gashi ne tare da Saurayinta, sai dai saurayin yayi tafiyarsa yayin da ake tsakar gyara ma Nathando gashi.

KU KARANTA: Ta rubuta Al-Qur’ani gaba daya da tawadan ruwan Zinari

Anci mutuncin wata budurwa dalilin Saurayinta

Ashe gogan naka alkawari ya dauka cewa zai biya kudin aikin idan ya dawo, sai dai fitar sa ke da wuya sai ya cika ma wandonsa iska, ba’a sake hango ko keyarsa ba.

Anci mutuncin wata budurwa dalilin Saurayinta

Nan fa budurwa Nathando tayi tsuru tsuru, inda har tayi kokarin tserewa, amma masu shagon suka kamata, sa’annan suka yanke gashin nata. Daga karshe suka yi mata dukan tsiya.

Za'a iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng