Aliko Ɗangote ya halarci bikin yaron babban dillalinsa
Shahararren attajirin nan dan Najeriya kuma shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya halarci auren wani yaron amininsa.
Bikin da Dangote ya halarta, aure ne na wani dan saurayi mai suna Ugochukwu Okika, wanda da yake a wajen hamshakiyar attajira Uwargida Beatrice Okika, wanda kuma itace babbar dillaliyar hajar simintin kamfanin Dangote.
KU KARANTA: Gwamnan jihar Osun ya kaddamar da makaranutun zamani
Ugochukwu ya auri tsohuwar budurwarsa Chinenye Nkeokelonye a garin Kalaba, sa’annan halartan Dangote bikin ya kara ma taron bikin armashi.
Bugu da kari an karrama Dangote a yayin bikin, inda aka nada shi uban taro, sai dai jama’a da dama da suka halarci bikin sunyi mamakin yadda Dangote ya dinga haba-haba da baki a yayin bikin.
Ga sauran hotunan bikin:
Zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng