Tony Anenih ya wallafa littafin tarihin rayuwar sa

Tony Anenih ya wallafa littafin tarihin rayuwar sa

Tsohon shugaban Jam’iyyar PDP Cif Tony Anenih ya bayyana yadda suka yi da Atiku Abubakar

- Anenih yace shi ya hana Atiku Abubakar tsayawa takara a shekarar 2003

- Wani dan siyasa mai murabus ya wallafa littafi game da rayuwar sa da siyasar kasar nan

Tony Anenih ya wallafa littafin tarihin rayuwar sa

 

 

 

 

Kwanan ne wani tsohon dan siyasar Kasar nan ya wallafa littafi game da Tarihin rayuwar sa da kuma siyasar Najeriya. Tony Anenih ya rike Shugaban Jam’iyyar SDP a lokacin Abiola, yana kuma cikin Manyan ‘Yan PDP kafin nan.

Tony Anenih ya sanar da cewa ya bar siyasa har abada, ya kuma nemi ‘yan Najeriya su marawa Shugaba Buhari baya wajen gyara Najeriya, duk da cewa Shugaba Buhari ya daure sa a zamanin da na wasu watanni.

KU KARANTA: Ana ta barin PDP a Gombe

Tony Anenih ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya nemi fitowa takara lokacin Cif Obasanjo yana neman komawa karo na biyu. Tony Anenih yace ya hana Atiku da ma wasu irin Tsohon Janar Babangida tsayawa takarar Shugaban Kasa, hakan kuwa bai ma su dadi ba.

Tony Anenih yace tun asali su suka fara bada sunan Atiku Abubakar a matsayin Mataimakin Shugaba Olusegun Obasanjo bayan an ci zabe a shekarar 1999.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel